Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Ibrahim Riza’i shugaban kwamatin Iran da Rasha na majalisun dokoki yana fadar haka a yau Lahadi. Ya kuma kara da cewa, daga ciki har da fitar da dalar Amurka a matsayin kudaden musaya a tsakaninsu.
Riza’ii ya kara da cewa a halin yanzu harkokin kasuwanci a tsakanin kasashen yankin Eurasia ya kai dalar Amurka biliyon $300, idan Iran ta sami ko kashi 10% na wannan harkokin kasuwanci zata sami alkhairi da yawa.
A makon da ya gabata ne shugaban kasar Iran ya ziyarci kasar Rasha, inda kasashen biyu suka kulla yarjeniyoyi da dama.
342/